
Kimanin yan Najeriya 117 ne suka makale a kasashe 3 na gabashin sakamakon annobar coronavirus wanda a yanzu suka dawo gida, kasashen da aka dawo sune Rwanda, Uganda da Tanzania.
Wadanda aka dawo dasu din an sauke su a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Lagos a safiyar lahadi.
Kamfanin jirgin saman Najeriya na Azman Air ne yayi jigilar mutane inda suka bayyana a shafinsu na Twitter suna yiwa wadanda jirgin nasu ya dauko barka da dawowa gida.

An yiwa wadanda suka dawo din gwajin cutar korona inda aka tabbatar basu da ita kafin a dauko su, haka nan an bukace su dasu killace kansu na kwanaki 14 kamar yadda kwamitin yaki da cutar da cibiyar NCDC suka kafa.
Haka nan ana sa ran zasu sake gwajin kafin su shiga cikin al’umma.
Shugabar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje Abike Dabiri-Erewa ta bayyana cewa fiye da yan Najeriya 6,000 ne aka dawo dasu daga kasashe 21 tun bayan barkewar cutar ta coronavirus.
