An Ceto Wata ‘Yar Najeriya Da Wani Dan Kasar Lebanon Ya Wallafa Zai Siyar

woman for sale in lebanon
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Hukumar yan Najeriya mazauna kasashen waje sun kubutar da wata mata yar Najeriya bayan da aka bugata a shafin sadarwa na Facebook kan ana neman mai sayenta a kan Dalar Amurka dubu daya ($1,000) a kasar Lebanon.

Matar na da kimanin shekaru 30 da haihuwa yar asalin jihar Ibadan dake yammacin Najeriya wadda a yanzu haka tana cikin koshin lafiya hannun hukumar wadda tuni suka kira dan uwanta dake Najeriya suka sanar dashi.

Hakan ya zo bayan da hukumomin kasar ta Lebanon suka kama mai tallan wato Wael Jerro inda suka ce hakan na cikin safarar dan Adam wanda kasar ta hana.

Jerro ya wallafa fasfo na matar a wani shafi na saye da sayarwa a kasar Lebanon kamar yadda aka dauki hoton shafin daga kafar sadarwar ta Facebook, inda ya wallafa da harshen Larabci.

“Ya bayyana cewa ga mai son mai aiki yar Najeriya mai shekaru 30, wadda take da kuzari da tsafta kudinta dalar Amurka dubu daya ($1,000)”.

Jami’an tsaron kasar ta Lebanon kasar bata amince a irin wan nan tallan ba don haka zasu kashi kotu.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply