An Bukaci Wasu Gidan Kafafen LabaraI Dasu Biya Ma’aikatan Su Hakokin Su

Wani kwararren dan jarida Dr Piman Hoffman ya kushe dibaan wadanda basu a korewa da wasu yan jaridu keyi wanda yace hakika hakan ya muzanta aikin jaridan Najeriya.

Dr Hoffman wanda mataimakin darakta da masu rohoton yanayi na Afirka yace a halin da ake ciki wasu kafafen labaran sun koma diban masu kiran su da sauran marasa korewa cikin aikin.

Ya kuma bayyana hakan yayin dayake zantawa da wakilin gidan rediyo Dandal Kura a Kaduna, Meyem Etim a lahadai da ake bikin yancin furuci nay an jarida.
Ya kuma shawarci kafafen labarai dasu guji aikata ayyukan kunya domin adana darajar aikin jaridar tare da cewa dole sai an hada hannu wajen tsame marasa korewa a cikin aikin.

Ya tuhumi wasu gidan jaridu masu zaman kansu da karfafa karanci biya dama ake hakkokin wasu inda ya bukace su dasubiya ma’aikata domin yabawa kokarin su tare kuma da basu dukkan ababen bukata dama horaswan domin sanin makaman aiki.