Amurka Tayi Allah Wadai Da Harin Filato

us small
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kasar Amurka tayi Allah wadai da hare haren da ake kaiwa a jihar filato dake najeriya inda kimanin mutane 94 suka rasa rayukansu da dama kuma suka samu raunuka.

Mai Magana da yawun rundunan tsaron amurka Ms Heather Nauert, tace yakamata adau mataki kan wadanda suka kai harin.

Kasar amurka ta yi Allah wadai da kakkaurar murya kan kisan mutane da kona musu dukiyoyinsu a Jihar filato a hutun mako.

Hakanan sun nuna rashin jin dadinsu na yadda ake samun karuwar rikice rikice akan mutane kuma tayi kira ga yan siyasa da manya mutane dasu sasanta matsalan dan akawo karshen wadan nan rikice-rikicen.

Ata bakin mai hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar filato Mr Terna Tyopev, ya bayyana cewa Fulani sun kona gidaje 50, motoci 2, Babura 15. Haka nan fulanin sun kewaye kauyukan Razat, Ruku, Nyarr, Kura and Gana-Ropp dake yankin Gashish a karamar hukumar Barkin Ladi inda akayi kashe-kashen.

Gwamnatin jihar ta sa dokar hana fita daga safe zuwa dare a Riyom da Barkin Ladi a Jos ta kudu bayan harin.

Haka nan shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar inda yayi alla wadai da harin kuma ya bayyana shi a matsayin abin takaici inda ya yace gwamnati zata dauki mataki.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply