
Inna Lillahi Wainnailaihirraji’un
An samu labarin rasuwar Malam Ibrahim El-hussain General Manager wato mai sa ido akan al’amuran gidan Radiyo Dandal Kura Radio International a safiyar yau
Malam Ibrahim El-hussain ya rasu yana da shekaru 61.
Ya jima yana aiki a harkan tace labarai sannan yayi aiki da kungiyoyi tace labarai da dama wanda ya hada kungiyar tace labarai ta kasa wato Nigerian Guild of Editors.
Ya rasu ya bar matarshi da yayanshi da kuma yan uwa maaza da mata.
Za’a yi jana’aizar shi Ayau A jihar kano.

Allah Yaji kanshi ya masa rahama.
Idan tamu tazo mu cika da imani.
Ameen
