Akalla Matasa Miliyan 2 Ne Suka Rasa Ayyukan Su Bayan Kafa Dokar Hukumar Sadarwa Na Kasa

NCC_LOGO
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Masu harkar wayoyin salula a yankin arewacin Najeriya sun ce akalla matasa miliyan 2 ne suka rasa ayyukan yi bayan kafa dokar hukumar sadarwa na kasa na hana sayar da layukan waya, da kuma yin rajista.

Kungiyar dilolin wayoyi na Arewa sun shaidawa manema labarai a jihar Kaduna cewa suna sane da shirin gwamnatin tarayya na magance matsolin rashin tsaro ta hanyar alakantawa da shaidar zama dan kasa da lambobin wayoyin, sai dai sun koka cewa suna shakkan matasa kusan miiyan 2 da suka rasa aikin yi ka iya kara matsalar tsaron

Shugaban kungiyar Hassan Yakubu, yace gwamnatin tarayya tane sane da kungiyar su kuma sun bada cikakken goyon baya ga matakin kare rayuka da dukiyoyin al’umma da gwamnatin ta dauka.

Ya kuma ce dole gwamnati sai ta karkatar da hankalin ta kan matasa domin bincike ya nuna rashin aiki na matasa shine ummul abasin duk matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta.
Yace yawan-yawan masu samun riba a kasuwancin wayoyin matasa ne yan shekaru 20 zuwa 40 kuma yace suna samu ne daga kasuwancin sayerwa da kuma rajistan layukan waya da suke yi.

Ya bada shawarar cewa, gwamnati ta bari aci gaba da sayar wa da kuma yin rajistar a lokaci guda kuma ta samar da na’urar NIN guda 10 a dukkan kananan hukumomi 774 na najeriya.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply