’aikatar Tarihi Da Al’adu Ta Kasa Ta Bayyana Cewa Taron Nuna Tsiraici Yafi Cutar Korona Illa.

images (65)
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Babban darakta janar na ma’aikatar tarihi da al’adu ta kasa Otunba Olusegun Runsewe yace taron nuna tsiraici da a yanzu yake yawo a kasa yafi cutar Korona muni.

Yayi kira gayan Najeriya da suyi watsi da wannan tsari na bata da kuma Allah wadai baki daya.

Ya bayyana haka yayin hirar sa da manema labarai.

Ya kara dacewa taron nuna tsiraici ba wai shigar da bayyana tsiraici bane da kuma rawa inda ya bayyana ta dacewa yafi cutar Korona muni.

Yace a misali maza da mata zasu hadu suna rawa suna juyi tare da aikata abinda bai dace ba kamar karnuka.

Yace a shekarar dubu 1 da dari 9 da 94 kasashen Gambia da Senegal sun dakatar da bude ido kan tsiraici shine kuma wasu a Najeriya da basu san muhimmancin al’ada bas uke son dawo dashi.

Daga karshe ya bukaci ministar al’amuran mata Mrs Pauline Tallen da ta shigo cikin lamarin, da kuma iyaye suyiwa yaran su gargadi kuma su koyar da su al’adun su.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply