Shugaban majalisar dattiwan Najeriya Ahmed Lawan yace yan Najeriya basua da wani zabi face ci gaba da marawa kasar da shuwagabannin ta baya dommin a samu damar shawo kan matsalolin rayuwa dana tsaro da ake fuskanta.
Yayin jawabi ga manema labaru ne ya bayyana hakan inda yace bai kyautu ba yadda wasu ke daurawa shugaban kasa ba bisa abubuwan dake faruwan kuma yayi kira ga dukkan shuwagabannin addinai, kabilu dama yan siyasa dasu fitar da maslaha ga matsalolin kasa.
Haka zalika yayi kira ga yan siyasan kasar dasu guji haddasa rarrabuwan kai da kalamai marasa dadi duk domi karfafa hadin kai a Najeriya .
Yace shugaba Buhari yana tuntubar dukkan masu ruwa da tsaki a Najeriya a aikin kare rayuka da dukiyan yan kasa kuma ya nemi dukkan shugabanni dasu marawa shugaban kasar baya
A game da kamala azumin water Ramadana, kakakin majalisar ya bukaci al’ummn musulmi da su kula da hakkokin juna.