Gwamna Zulum Ya Tallafawa Kungiyoyin Fararen Hula Da Miliyan 5

zulum (15)
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya tallafawa kungiyar fafaren hula reshen jihar da naira miliyan 5 don tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a taron da aka gudanar na zaman lafiya a yankin Arewa maso gabas da aka gudanar a Maiduguri.

Shugaban ma’ikata na fadar gwamnan jihar farfesa Isa Marte ne ya wakilci gwamnan inda yace babu kasar data cigaba ba tare da zaman lafiya mai dorewa ba.

Haka nan yace a kasashen da suka cigaba akwai rikice rikice dake son durkusar da tattalin arzikinta.

Acewar sa hanya day ace kasa zata cigaba idan tana da gwamnati mai kyau da inggganci wadda ke ayyukanta a bayyane.

Shugaban kungiyoyi masu zaman kansu reshen jihar Adamawa State Peter Egwudah a takardar day a gabatar yace ya kamata a duba abubuwa 3 wajen farfado da zaman lafiya a yankin wanda suka hada da sasantawa day an kungiyoyin.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Related stories

Leave a Reply