A yau litinin Kotun koli ta tabbatar da sakamakon zaben gwamna Abudullahi Ganduje na jihar Kano.

court
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kotun kolimai wakilai 7 wadda babban jojin Najeriya wanda justice Tanko Muhammad ke shugabanta, ta kori karar da dan takarar jam’iyyar PDP Abba Yusuf ya daukaka gabanta inda yake kalu balantar sakamakon zaben gwamnan jihar Kano daya gabata.

A karar da Abba Yusuf ya daukaka, ya roki kotun kolin data soke hukuncin da kotun sauraran korafe-korafen zaben gwamnan jihar kano da kuma kotun daukaka kara suka yanke inda suka amince da sake zaben Dr Abdullahi Umar Ganduje.

Yace shi ne ya samu kuri’i mafi rinjaye a zaben gwamnan da aka gudanar a ranar 9 ga watan marisna 2019 kamar yadda sashe na 179 karamin sashi na 2 na kundun tsarin mulki na shekarar alip dari 9 da casa’in da tara da akayiwa gyara ya tanada.

Cikin takaddar daukaka kara daya shigar a ranar 30 ga watan nuwanban 2019, yace bayan da baturen zabe na jihar Kano ya fadi sakamakon zaben kananan hukumomi 44, ya soke na rumfunan zabe 207 inda ya bayyana cewa, zaben be kammalu ba wanda aka sake gudanar dashi a ranar 23 ga watan maris na 2019.

Sede kuma a hukuncin da kotun kolin ta yanke wanda mai shariah Sylvester Ngwuta ya karanta, kotun tace babu wani kwararran dalili da zai sa a watsar da hukunci da kotunan bayan suka yanke.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Related stories

Leave a Reply