A Ranar Asabar Kasar Najeriya Ta Cika Shekara 1 Da Samun Bullar Cutar Corona Virus.

NCDC
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Cibiyar hana yaduwar cututtuka ta kasa tace an samu sabbin masu dauke da cutar Korona a ranar asabar da suka kai 341 wanda ya kama adadin masu cutar dubu dari 1 da 55 da dari 4 da 17 tun bullar ta a ranar 27 ga watan Fabrairun shekarar 2020.

Cibiyar ta bayyana haka ta shafin ta na Twitter a daren asabar.
Rahotanni ya nuna cewa a ranar asabar kasar Najeriya ta cika shekara 1 da samun bullar cutar.

Ya zuwa yanzu da ake da masu cutar da suka kai dubu dari 1 da 55 da dari 4 da 17, an sallami mutane dubu dari 1 da 33 da dari 2 da 56 sannan dubu 1 da dari 9 da 5 sun rigamu gidan gaskiya a dukkan jihohi 36 hade da birnin tarayya.

Cibiyar tace an samu masu cutar a jihohi 20 da babban birnin tarayya.
Jihohin da aka samu masu cutar akwai jihar Lagos-96, Rivers-41, Kaduna-33, Edo-21, Osun-20, Akwa Ibom da babban birnin tarayya suna da-17.
Sauran sun hada da Ondo 15; Gombe- da Kano-11; Imo-10; Ekiti da Kebbi 9; Kwara da Oyo 8; Borno 6; Enugu da Plateau 3; sai kuma Delta, Naija da Ogun suna da daidaya.

Cibiyar ta kara da cewa a yanzu ana da masu cutar da suka kai dubu 20 da dari 1 da 83 a jiya.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply