
Hukumar kula da 6arkewar cututtuka na tarayyar Najeriya ta gayyaci ‘kwararru a’kalla 200 domin daukar matakan domin magance matsalar 6arkewar cututtuka a ‘kasar.
Taron wadda aka fara ranar Litinn da ta gabata ta maida hankali ne kan kare lafiyar fararen hula a ‘kasar.
Hukumar ta bayyana cewa taron zata baiwa ‘kwararrun, damar fito da sabbin dabaru da za ta taimaka wajen inganta shaanin kiwon lafiya a ‘kasar.

Yayin taron an tattauna batutuwa da dama da suka shafi kiwon lafiya, wadanda suka hada da yadda za a dakile wasu cututtuka ciki har da cutar Ebola, ‘kyanda da cutar amai da gudawa.
Daga cikin bakin da aka gayyata a wajen taron, akwai ‘kwararru daga ‘kasashen Uganda da kuma Liberia.
