A Karon Farko An Samu Wani Shugaban Yan Aware A Kasar Kamaru

cameroon
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

A karo na farko an samu wani shugaban yan aware na kasar kamaru wanda ya fito fili ya bayyana cewa hakika mayakansa na tabka rashin mutunci ga jama’an yankin harshen turanci.

Shugaban Awaren, Lucas Ayaba wanda a yanzu haka ya samu shaidar zama dan kasar Norway ya wallafa a kafar sadarwa cewa mayakan sun mayar da gogormayan yakin neman yancin zuwa abin kunya wanda yace yaji kunya kwarai da daya daga cikin mayankasa ya mutu a dalilin dabanci.

Kungiyoyin kare rajin bil’adama da dama sun alakanta alhakin garkuwa da mutane, da azabtarwa, kasha-kashe da sauran su ga yan awaren hade da dakatar da zuwa makarantu da kisan malamai.

Babban limamin kristoci na majami’ar katolika a kasar Kamaru Cardinal Tumi, yace a yan kwanakin nan yan awaren sun lalata tattalin arzikin yankin turancin bayan kai farmaki da cin zarafin manoma da suka fita aiki domin rufawa kansu asiri.

Cardinal Tumi yace a dalilin iren-iren keta haddin na ne ya sanya da dama cikin jama’an yankunan harshen turanci na arewa maso yammaci da kudu maso yammacin kasar suke adawa da yan awaren.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply