A Kalla Mutane Dubu 75 Suka Amfana Daga Ciyarwar Watan Ramadan Na Gwamnatin Kihar Kano A Kullum.

A kalla mutane dubu 75 ne suke amfana daga ciyarwar da akei na watan Ramadan daga gwamnatin jihar Kano a cewar Abubakar Kofar Naisa mai taimakawa gwamna Abdullahi Ganduje na musamman kan harkokin yada labarai.

Acewar mai taimakawa gwamnan wanda kuma jami’in yada labarai na kwamiin rabon abincin, cikin wata sanarwa da aka fitar ya nuna cewa ana gudanar da hakan a cibiyoyi 150 kullum a fadin kananan hukumomi.

Ya kara dacewa tun shekarar 2015 gwamnan ya kara cibiyoyi domin mutane su amfana da shirin.

Yace mambobin kwamitin suna dubu yanayin aikin domin tabbatar da an raba yadda ya dace.

Ya bayyana cewa manufar su shine ganin wadanda suka dace su samu sune suke amfana daga shirin domin rage musu radadin da suke ciki.

Wakilin shugaban kwamitin Mal. Abba Yakubu ya nuna gamsuwar san a yadda ake sarrafa abincin da kuma rabawa ga mabukata.

Kuma yayi amfani da wannan dama wajen kira ga masu hannu da shuni wajen taimakawa gwamnatin jihar Kano na ciyar da mabukata musamman a wannan wata na Ramadan.

An kaddamar da rabon abincin ne a ranar 13 ga watan Afrilu kuma ana sa ran zai kai har karshen watan Ramadan.