Shugaba Buhari Ya Bukaci A Rabawa Manoma Kayan Noman Da Aka Gyara

buhari
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci Hukumar Kula da Kayan Kimiyya da aikin Injiniya ta kasa da ta tura taraktocin da aka gyara ma manoma domin bunkasa ayyukan noma a kasar.

Mataimakin Shugaban Hukumar Kula da Kayan Kimiyya da aikin Injiniya Farfesa Mohammed Sani Haruna ne ya shaida wa manema labarai na Fadar Shugaban Kasa cewa Shugaban ya ba da umarnin ne bayan karbar bayanan ayyukan hukumar a ranar Laraba a Fadar Shugaban Kasa dake Abuja.

Haruna ya ce umarnin na shugaban kasar yayi daidai da kokarin da gwamnatin Shugaba Buhari take yi na sake fasalin bangaren noma.

Shugaba Buhari a ranar 29 ga Disamba ya tabbartarwa ‘yan Nijeriya cewa gwamnatin sa za ta sa ido sosai kan hauhawar farashin kayan abinci a cikin Sabuwar Shekarar.

Shugaban Hukumar Kula da Kimiyyar ya ce ya yi wa Shugaban kasar karin bayani a kan nasarorin da hukumar ta samu.

Haruna ya lissafa nasarorin da Hukumar Kula da Kimiyya ta Kasa ta samu wanda ya hada da kera keke mai kafa uku wanda zai dauki fasinjoji da kaya.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply