borno-state-small
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Yan kasuwa a jihar Borno sun yaba da shugaba Buhari a game da umarnin da ya bada na bude kan iyaka hudu.

Alh Abba Ganama wani dan kasuwa dake birnin Maiduguri ya fadawa gidan Radiyo Dandal Kura Radio cewa bude kan iyakar yazo dai-dai a wannan lokaci.

Dandal Kura Radio International ta bayyana cewa shugaban Buhari ya bada umarnin ne a shafin offishin shugaban kasa na tweeter a jiya laraba.

Shugaba Buhari ya bada umarni da a gaggauta abude kan iyaka hudu wanda ya hada da iyakar Seme, Illela, Maigatari, da kuma Mfun

Kasar Nigeria ta kulle kan iyakan a watan Augusta cikin shekarrar 2019 domin dakatar da shigowa da harramtattun makamai,miyagun kwayoyi, da kuma kayakin abinci da basu dace ba .

Ministan kudi da kuma tsare-tsare ta kasa Zainab Ahmed ta bayyana cewa kwamiti masu aiki a wannan bangaren sunce sungama ayyukan da sukeyi kuma za’a iya buda kan iyakan a yanzu.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply