Shugaban Kasar Najeriya Ya Koka Kan Karin Da Yan Majalisa Suka Yiwa Kansu

Buhari
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu buhari ya rattaba hannu kan kasafin kudi na 2018, sai dai kuma shugaban ya nuna rashin jindadi sa dangane da rage wasu kudaden da yan majalisa sukayi wanda yawan su yakai N347B wanda aka ware domin yin wasu manyan aYyuka ciki har ma da aikin tashar samar da wutar lantarki na mambilla.

Sai dai kuma shugaban ya koka kan wani kari da yan majalisar sukayi na kudaden da aka ware musu tun farko da yawansu yakai N578B.

Bayan yan majalisar sunyi wa kasafin kudin garanbawul, kasafin kudin ya tashi daga N8.612 zuwa N9.120.

A lokacin da yake rattaba hannu akan kasafin kudin, shugaba buhari ya bayyana cewa, la’akari da sauye-sauye da yan majalisar sukayi wa kasafin kudin, zaiyi wuya asamu a kammala wasu manyan ayyuka da aka kudiri aniyar yi tun farko.

Ya kuma zargi yan majalisar dayin sara ba tare da suna duba bakin gatari ba.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply