Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Gwanonin Yankin Arewa Maso Yanma Sunrufe Makarantu Sakamakon Cutar Covid 19

northern-nigeria
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnonin yankin arewa maso yamma sun bayar da sanarwar rufe dukkan makarantunsu na tsawon kwanaki Talatin.

A sanarwar bayan taron da Shugaban kungiyar Gwamnonin yankin kuma Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Masari ya karantawa manema labarai yace daukar wannan mataki ya zama wajibi domin kare bazuwar cutar Corona Virus ko kuma Covid 19 a yankin na arewa maso yamma.

A ranar labara ce aka samu rahoton bullar cutar a karfon farko a yankin a jihaar Katsina.

Gwamnonin sun taru ne a Kaduna tare da Shugabannin Hukumomin tsaro dake yankin domin duba dabarun da za’a sake bi wajen yaki da barayin mutane kafin daga bisa ni a samu rahoton bullar cutar Corona virus a Katsina.

Gwamna Masari yace za’a rufe makarantun ne daga ranar litinin ashirin da uku ga watan nan na Maris.

Yace Gwamnonin za kuma su zauna da Hukumomin shirya jarrabawa domin tattaunawa kan matakin da za’a dauka kan jarrabawar da suke shiryawa.

Ya kuma shawarci jama’a da su gujewa yin tarurrruka da ba su zama dole ba sannan su dauki matakai na kare bazuwar cutar Covid 19.

Leave a Reply