Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Gwamnonin Najeriya Sun Tabbatar Da Ingancin Rigakafin Na Astrazeneca

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnonin Najeriya sun tabbatar da cewa rigakafin ta Astra Zeneca vaccines nada inganci.

Hakan na cikin abunda suka yanke wanda shugaban kungiyar Gwamnonin Kayode Fayemi na jihar Ekiti yasa hannu a karshen taron da suka gudanar karo na 28 ranar Laraba a Abuja.

Gwamnonin sun tattauna kan abubuwan da suka shafi kasar mussaman kan rigakafin COVID-19da sauran batutuwa.

Haka nan Fayemi ya taya takwarorin sa dangane da yadda da karbar allurar da sukayi inda yace har yanzu allurar bata da wata illa.

San nan kungiyar ta kara da cewa kwamiti kan cutar da suka kafa wanda farfesa Oyewale Tomori yake jagoranta ya bayyanawa ggwamnonin yadda ake karbar rigakafin a jihohin.

Haka nan yace ya kamata yan Najeriya su gaba da karbar allurar AstraZeneca kamar yadda kungiyar lafiya ta duniya ta umarta.

Gwamnonin sun sun karfafawa mutane gwiwa kan rigakafin na COVID-19.

Leave a Reply