Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Gwamnonin Arewa Maso Gabas Sun Kirayi Shigowar Matasa Cikin Gwamnati.

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnonin arewa maso gabas, wadanda aka zaba a karkashin jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ranar asabar, sun gabatar da hujja mai karfi ga shigar matasa cikin shugabanci.

Sun bukaci gwamnati a dukkan matakai data ba matasa da mata kashi 50 na zabbabun mukamai da nade-naden.

Gwamnonin, sanata Bala Abdulkadir Mohammed (Bauchi); Ahmadu Umaru Fintiri (Adamawa) da Darius Dickson Ishaku (Taraba) sunyi wannan ikirarin ne a jawaban su daban -daban a taron matasan PDP na arewa maso gabas.

Taron, wanda ya samu wakilai daga adamawa, Bauchi, borno, gombe, Taraba da yobe sunyi taken ‘matasa a cikin shugabanci’ kuma an gudanar da shi a multi-purpose hall Bauchi.

Da yake jawabi, gwamna mohammed ya bayyana cewar don najeriya ta cigaba, bazata iya cigaba da sake dawo da shugabanninta ba.

A cewarsa akwai matukar bukatar kasar ta bude sabbiniyakoki da kuma gano sabbin abubuwa da kare-kare, wadanda yace kawai za’a iya gano su a cikin matasa.

Gwamnan ya koka kan yadda acikin shekaru shida da suka gabata, an mayar da matasa koma baya a shirin aiwatar da abubuwa a harkokin Mulki, yana mai cewa wannan ya saba da abin da’aka samu lokacin da PDP ta kwashe shekaru 16 tana mulkin kasar

Leave a Reply