Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Gwamnatin Tarayya Tace Tanada Niyyar Saida Man Fetur AKan Kasa Da Naira 100.

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa muhammadu Buhari kan harkokin Neja Delta, sanata Ita Enang, yace gwamnatin tarayya na da niyyar sayar da mai a kasa naira 100 a kowace lita.

Hadimin shugaban kasar ne ya bayyana hakan a wani taron manena labarai a abuja.

Enang, wanda yayi magana a ranar laraba a taron kasa da aka shirya kan hada ayyukan matatar mai ta zamani don inganta karfin kayayyakin mai, yace gwamnatin Buhari na aiki tukuru don inganta rayuwar yan najeriya.

Yace taron, wanda za’a gudanar a ranar 16 da 17 ga maris, 2021, za’a gudanar da shi ne daga fadar shugaban kasa tareda hadin gwiwar ma’aikatar kudi ta tarayya, kasafin kudi da tsare-tsaren kasa.

Yace, sakamakon taron zai tattara dukkanin kadarorin najeriya, wadanda suka hada da masu fasaha, injiniyoyi, masu kera albarkatun man fetur a kogunan Naje Delta da sauran lamuran da suka dace, inda ya kara da cewa, yayin da farashin danyen mai ya tashi sama, amma idan aka tsaftace kayayyakin man fetur a Najeriya, kudin zaiyi kasa sosai.

Leave a Reply