
Karamin ministan lafiya Dr. Adeleke Mamora yace gwamnatin tarayya bazata tursasa kowani dan kasa ba wajen karbar rigakafin cutar corona, sai dai ya bukaci jama’a don son kan su.
Ya bayyana haka a Asaba babban birnin jihar Delta yayin kaddamar da ayyuka a cibiyar lafiya na tarayya.
Ayyukan sun hada da dakin gwaje gwaje, dakin kula na musamman guda 15, rukunin gidaje da gidan sauke baki.

Ya yabawa darakta janar na cibiyar hana yaduwar cututtuka ta kasa bisa samar da kayaki da kudade wajen gyare gyare a asibitin.
D
Daraktan cibiyar lafiya na tarayya Dr. Osiatuma Victor yace a jawabin sa, an samar da asibitin ne a watan Agusta na shekarar dubu 1 da dari 9 da 98 wanda yam aye gurbin tsohon kwararren asibiti na Asaba.
