Gwamnatin Tarayya ta bayyana kafa Hukumar tsaro ta Operation Amotekun da cewa baya bisa doron doka.

GwamnatinTarayya ta bayyana Hukumar tsaron da jihohin dake yammacin Najeriya suka kafa mai suna Amotekun da cewa baya bisa ka’ida.

Antoni Janaar kuma Minisstan shari’a, Abubalaar Malami  shine ya bayyana hakan a sanawar da aka bayar yau da safe.

Sanarwar wacce Mai bashi shawara na musamman kan kafofin yada labarai, Dr. Umar Gwandu ya sanyawa hannu yace kafa Hukumar ya sabawa doka.

Sanawar ta kara da cewa kafa Hukumar tsaron ta Amotekun ba ya bisa kaa’ida sannan ya sabawa dokokin Najeriya.

Kudin tsarin mulkin Najeriya na shekara ta1999 da aka yiwa gyara, ya tanadi kafa rundunar sojan kasa, da ta sojan ruwa, da kuma ta sojan sama, da Hukumar ‘Yan sanda da sauran Hukumomi na masu sanya kayan sarki domin tsaron Najeriya.

Sanarwar tace Antoni Janar na Tarayya yace babu wata jiha ko jihohi da zasu taru su kafa ko wacce irin Hukumar tsaron Najeriya ko tsaron wani bangare na kasar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *