Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranar 2 Da 5 Ga Watan Afrilu A Matsayin Hutun Easter

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Juma’a 2 da Litinin 5 ga Afrilu 2021, Ranakun hutu don bikin Bikin Ista na wannan shekara.

Ministan cikin gida, Ogbeni Rauf Adesoji Aregbesola, wanda ya bayyana hakan a madadin Gwamnatin Tarayya, inda ya bukaci Kiristocin da su yi koyi da halaye na hakuri, yafiya, alheri, kauna, zaman lafiya da hakuri, kamar yanda Yesu ya nuna.

Ya yi kira a gare su da su yi amfani da wannan lokaci na Bikin Ista na wannan shekara don yin addu’a don zaman lafiya, Hadin kai, da Ci gaban kasarmu.

Aregbesola ya ba da tabbacin cewa Gwamnatin Tarayya ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen shawo kan matsalar satar mutane, fashi da makami da sauran laifuka da makiya kasar ke aikatawa a sassan Najeriya.

Ya ce tsaro hakkin kowa ne, don haka dukkan ‘yan Najeriya da baki da ke zaune a Najeriya ya kamata su nuna kishin kasa a wannan mawuyacin lokaci mai tarihin da kasar ke ciki don tallafawa kokarin dukkanin hukumomin tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyar yan kasa.

Yayin da yake yiwa mabiya addinin kirista na gida da na waje murnar bikin Easter, Aregbesola ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su hada kai da Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kokarin ta na ganin kowa ya samu rayuwa mai inganci.

Leave a Reply