Gwamnatin Tarayya Da Kungiyar Likitoci Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniya Domin Kawo Karshen Yajin Aiki.

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnatin tarayya ta sanya hannu kan yarjejeniya tsakanin ta da kungiyar likitoci wadanda suke yajin aiki domin ganin an kawo karshen yajin aikin da suke.

Wannan yarjejeniyar shine karo na biyu, na farko an sanya hannu a ranar 31 ga watan Maris daga bisani likitocin suka ki amincewa da shi.

Ministan kwadago da ayyuka Sanata Chris Ngige have yarjejeniyar da akan sanya hannu a Abuja ya zone bayan taron amincewa tsakanin gwamnatin tarayya da likitoci.

Yace taron da aka gudanar ya zama dole a gyara yarjejeniyar da aka sanya hannu na farko tare da likitocin.

Yace akwai rashin daidaito a cikin tsarin biyan albashi na likitocin inda yace wasu an biya su sau biyu wasu kuma basu samu nasu ba har yanzu.

Sakamakon hakan an nada kwamiti mai mutane 5 domin fitar da sunayen wadanda abin shafa tsakanin a wanni 72 domin mika takardan ga tsarin biyan albashi na IPPIS ta hannun ma’aikatar lafiya ta kasa.

Ya kara dacewa shugaban kwamiti kan biyan albashi zai gana da hukumar kudaden shiga da albashi a ranar 12 ga watan nan kan matsalolin alawus nasu.

Haka kuma bangaren kungiyoyin lafiya da kungiyar likitoci da sauran masu ruwa da tsaki zasu gana a ranar 14 ga watan nan.

Daga karshe shugaban kungiyar Dr. Uyilawa yayi alkawarin bayyana yarjejeniyar da sukayi ga mambobin su domin kawo karshen yajin aikin da suka fara a ranar 1 ga wannan watan.

Leave a Reply