Gwamnatin Taraiya Ta Rage Farashin mai Fetir zuwa Naira Dari Da Ashirin Da Biyar

nnpc-small
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnatin Tarayya ta umarci Kamfanin man fetur na kasa NNPC da ya daiddaita farashin man da yake sayarwa jama’a domin ya yi daidai da yadda farashinsa yake yanzu  a kasuwar duniya..

A bayanin da Majalisar zartarwa ta Tarayya ta yi, tace yanzu farashin litar man zata koma Naira dari daya da ashirin da biyar.

Shugaban kasa ya bayar da umarnin sauko da farashin man ba tare da wani jinkiri ba.

Karamin Ministan man fetur, Mr. Timipre Sylva wanda ya bayar da umarnin a madadin Shugaban kasa, ya shaidawa manema labarai cewa Kamfanin Mai na kasa NNPC da kuma Hukumar daidaita farashin albarkatun man fetur ta PPPRA zasu sanya ido domin tabbatar da ganin Masu gidajen mai su kiyaye da wannan umarni.

Har’ila yau yace ma’aikatarsa zata dauki matakai na ganin farashin albarkatun Man sun tafiya daidai da yadda farashinsu yake kasancewa a kasuwa.

Ministan yace wannan mataki zai tallafawa bangaarorin tattalin arziki tare da samarwa ‘Yan Njeriya rangwame sannan zai share hanyar samar da wadataccen Man a Najeriya.

Mr. Sylva yace a makon jiya ne Gwamnaati ta tuntubi masu ruwa da tsaki game da yiwuwar rage farashin Man sakamakon faduwar darajar Danjen Man a kasuwar duniya.

Leave a Reply