Gwamnatin Najeriya Zata Samar da Kudade Kan Masu Cutar Lassa

Gwamnatin kasar Najeriya zata samar da kudaden da za’a kula da masu dauke da cutar Lassa fever a kasar, inji Darakta Janaral na hukumar kula da cututtuka wato Dr. Chikwe Ihekweazu.

Ya bayyana cewa za’a samar da kudaden ne don ganin kudi bai kawo tsaiko ba kan kula da masu dauke da cutar Lassa fever.

Ya kara da cewa suna nan suna gudanar da shirye-shirye a matakan bada magunguna matakin farko don a biya kudin maganin masu dauke da cutar ta Lassa fever, gwamnati na nan tana tattaunawa don ganin an shawo kana abun.

Ihekweazu ya kirayi yan Najeriya dasu dauki duk wasu matakai da zasu kawo karshen ciwon kamar su kula da guraren ajiye abinci da gyara mahallinsu.

Haka nan ya kara da cewa basai masu hannu da shuni ne kadai zasu kula da mahallinsu ba, saboda haka ya kamata ayi amfani da yarurrukan da ake dasu a Najeriya a fadakar da jama’a kan yadda zasu kare kansu daga ciwon.

Ribalvrin magani ne mai matukar tsada amma gwamnati zata yi kokari taga ta bada maganin kyauta ga jama’a, kuma ya kamata jama’a su kare kansu daga wan nan ciwon.

NCDC ta kirayi al’umma dasu kare kansu saboda duk yadda za’a baka magani baka da tabbas kan abinda zai faru, kare kai shine gaba da komai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *