Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Gwamnatin Najeriya Tace Ta Biya Naira Miliyan 200 Ga Hukumar Jarrabawa Ta NECO

NECO
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnatin Najeriya tace ta biya Naira miliyan 200 ga hukumar jarrabawa ta kasa wato National Examination Council don sakin sakamakon jarrabawar dalibai 30,000 wanda hukumar ta rike musu sakamakon.

Rahoton ya fito daga sakatariyar gwamnan jihar Niger Abubakar Bello, inda ta bayyana a garin Minna cewa kudin na cikin wani kaso da hukumar take bin jihohin arewa ta tsakiya.

An bayyana cewa gwamnatin ta biya fiye da Naira biliyan daya ga hukumomin jarrabawar da dama a shekara 3 da suka gabata a kokarinta na bada ilimi kyauta ga daliban jihar.

Rahoton ya kara da cwa gwamnatin jihar ta yadda kan cewa zata dinga biyan hukumar jarrabawar Naira miliyan 50 a ko wane wata don ta kammata biyan kudaden da ake binta.

Haka nan gwamnatin jihar ta gana da ma’aikatan NECO, inda suka tabbatar cewa bayan biyan wasu kudade zasu saki sakamakon jarrabawar cikin sati.

Related stories

Leave a Reply