Gwamnatin Najeriya Ta Bada Laraba A Matsayin Hutun Ranar Damokaradiyya

Gwamnatin Najeriya ta bayyana ranar Laraba a matsayin hutun ranar damokaradiyya ta kasa. Sakatariyar din-din-din ta ma’aikatar cikin gida Georgina Ehuriah ce ta bayyana hakan a rahoton data fitar ranar Litinin ta bakin mai Magana da yawun ma’aikatar Mohammed Manga.

Cikin rahoton Mrs Ehuriah tace tana taya yan Najeriya na gida da mazauna waje muranar ranar damokaradiyyar ta Najeriya.

Haka nan ta kirayi dukkanin yan Najeriya da su bada goyon baya ga gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari don samun hadin kai, zaman lafiya da cigaban tattalin arzikin kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *