
Gwamnatin kasar Najeriya ta bayyana ranar laraba 1 ga watan mayu a matsayin hutu don gudanar da hutun ranar ma’aikata ta shekarar 2019.
Ministan cikin gida Abdulrahman Dambazau ne ya bayyana hakan a madadin gwamanatin tarayyar kasar, inda gwamnatin ta yabawa ma’aikatan kan kokarin da suke na gina kasar.
Dambazau ya bayyana hakan a sakon da ya fitar ranar litinin a Abuja ta bakin sakatariyar ma’aikatarsa Mrs Georgina Ehuriah.

Haka nan yay aba wa ma’aikata a kokarin da suke na ganin an tabbatar da ayyukan da gwamnati take gay an kasar da kuma yan kasashen waje.
Dambazau ya godewa yan Najeriya kan yadda suke bawa gwamnatin shugaba Buhari hadin kai wajen gina Najeriya.
A karshe Ministan yayiwa yan Najeriya fatan alheri da gudanar da bikin ranar ma’aikatan lafiya.
