Gwamnatin Najeriya Ta Bada Hutu Talata Da Laraba Don Bikin Sallah Karama

BY: YABAWA ISMAILA BORNO

Gwamnatin kasar Najeriya ta bada hutu ranar Talata 4 ga watan Yuni da Laraba 5 ga watan Yuni don gudanar da bikin sallah karama.

Sakatariyar din-din-din ta hukumar cikin gida Barrister Georgina Ekeoma Ehuriah ce ta bayyana hakan a rahoton da daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar Mohammed Manga yasa hannu.

Ta taya musulmin najeriya murna da kuma gama azumin na Ramadan cikin nasara inda ta bukaci yan najeriya dasu yi amfani da lokacin wajen addu’oi ga kasar na zaman lafiya da hadin da cigaba.

Haka nan ta bukaci yan Najeriya dasu kaucewa maganganun batanci ga juna kuma su hada kai su bawa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari hadin kai don a gina kasar cikin hadin kai da cigaba inda za’a kaita mataki na gaba.

Barr. Ehuriah ta tabbatar da kokarin gwamnati wajen ganin ta kare mutane da dukiyoyinsu yayin bikin sallah karamar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *