Gwamnatin Najeriya Ta Bada Hutu Ranar Laraba 29 Ga Watan Mayu

By: Adamu Aliyu Ngulde

Gwamnatin kasar Najeriya ta bada hutu ranar laraba 29 ga watan Mayu 29 don mika Mulki ga sabuwar gwamnati a shekarar 2019.

Rahoton ya fito daga sakatariyar dindin din ta hukumar cikin gida Georgina Ehuriah. Ehuriah ta bayyana cewa Ministan cikin gida Abdulrahman Dambazau ne ya bayyana hakan a madadin gwanatin tarayya, inda yace yana taya shugaba Muhammadu Buhari murnar sake lashe zabe karo na biyu kuma yana yiwa yan najeriya murnar gama zaben 2019 lafiya.

Haka nan ya kirayi yan Najeriya da su bada hadin kai ga gwamnatin da zata kama aiki wanda hakan zai kawo cigaban kasa da habbaka rayuwar jama’a, hadin kai, da cigaban kasa zuwa mataki na gaba.

Ya kara da cewa da hadin kan yan Najeriya kasar zata canzu a shekaru 4 masu zuwa inda har wasu kasashen zasuyi kishinta.

Ministan yayi wa gwamnati fatan alkhairi na yin Mulki cikin kwanciyar hankali, ya kara da cewa duk da an maida rnar Damokaradiyya ranar 12 ga watan Yuni za’ayi bikin rantsarwa ranar 29 ga watan Mayu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *