Gwamnatin Jihohin Borno Da Yobe Sun Ki Amincewa Da Yan Sandan Jiha.

Gwamnatin jihohin Borno da Yobe sun ki amincewa da kara samar da majalisar yan sanda na jihohi da kananan hukumomi a kasa.

Jihohin biyu sun bayyana ra’ayin su cikin bayani daban daban yayin dubu kundin tsarin kasa a jihar Bauchi.
Kakakin majalisar dokokin jihar Borno Alh. Abdulkareem Lawan yace jihar bata amince da samar da karin yan sanda na jihohi da jiha ba.

Yace tuntuni jihar Borno ta galabaita, basa bukatar karin wasu majalisu dan wasu kawai suna nan ne, dan haka basa bukatar samar da jiha ko kananan hukumomi.

Haka ma a bangaren kara samar da yan sandan jiha, kakakin majalisar dokokin yace ba’a bukatan haka domin gwamnatin jiha ta samar da jami’an sa kai na CJTF domin habbaka tsaro a jihar.

Kuma yayi kira kan daidaiton jinsi da kuma kara mata a bangaren gwamnati da kuma marasa karfi.

A nashi bangaren attoney janar kuma kwamishinan shari’a na jihar Yobe Saleh Samanja ya amince da dakatar da samar da jihohi da kananan hukumomi.

Yace a inganta jihohi a kananan hukumomi wadanda ake dasu a kasa a yanzu, yace majalisun basa samun isashen kudade domin aiwatar da ayyukan cigaba.


A bagaren yan sanda kuma yace hakan zai kara matsalar rashin tsaro, a maimakon haka a inganta yan sanda na al’umma.