Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Gwamnatin Jihar Gombe Ta Dauki Yara Dubu Dari Biyu Da Goma Sha Fudu A Makarantun Gwamnati.

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

A kokarin Gwamnatin jihar Gombe na rage yawan yaran da suka daina zuwa makaranta, ta dauki Yara dubu 214 a makarantun Gwamnati daga watan Satumba na bara zuwa watan Janairu na bana.

Gwamnan jihar Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya shine ya bayyana hakan lokacin da yake kaddamar da shirin raba rigunan makaranta da sauran kayan karatu ga ‘yan makarantun Firamare wanda aka gudanar a makarantar Firamare ta Jalingo Ashaka dake yankin karamar Hukumar Funakaye.

Gwamnan yace kayan sawa na makaranta da kuma Jakunkuna da sauran kayan rubutu za’a raba musu ne ga ‘Yan makarantun Firamare da cibiyoyin koyar da ‘Yan mata na Gwamnati a karkashin shirin Gwamnatin Tarayya na samar da ilimi ga kowa.

.Gwamnaa Inuwa Yahya yace akwai Almajirai dubu 70 da aka shigar da su tsarin bayar da ilimi na zamani da kuma ‘Yan mata dubu 40 da su kuma aka sanya su cibiyoyin koyawa  dake jihar.

Yahaya .Yace a lokacin da ya karbi mulkin jihar a bara akwai Yara sama da dubu 500 da suka daina zuwa makaranta gami da tarin matsaloli da suka dabaibaye makarantu.

Yace  zuwa yanzu Gwamnatinsa ta kashe Naira miliyan dubu biyu da miliyan dari tara wajen gyara ajujuwa 400 na makarantun Firamare da na Sikandire dake jihar.

Shi kuwa Shugaban Hukumar ilimin bai daya na jihar, Alhaaji Babaji Babadidi yace an zabi kaddamar da shirin rabon kayayyakin makarantar ne a karamar Hukumar Funakaye saboda la’akari da cewa tana daya daga cikin yankunan da suke da yawan ‘Yan makaranta a jihar Gombe.

Shi kuma Jami’in Hukumar bunkasa ilimi a makarantu ta jihar, Dr. Abdullahi Ahmad kira yayi ga Iyayen yara da su baiwa Gwamnati cikakken hadin kai ta hanyar sanya ‘ya’yansu a makarantar tare da ganin su kammala.

Dr. Abdullahi Ahmad yace an samu nasarar shirin ne sakamakon goyon baya da Shugabannin al’umma da na addini ke bayarwa.

Leave a Reply