Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Gwamnatin Jihar Adamawa Zata Kammala Ayyukan Da Ba’a Gama Ba A Jihar

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

By Hassan Umar Shallpella, Adamawa
Kwamishinan Yada Labarai da Dabaru na jihar Adamawa Kwamared Umar Garba Pella ya jaddada aniyar gwamnati na kammala duk ayyukan da aka fara a jihar wadanda tsohuwar gwamnatin ta bari a jihar.

Kwamared Pella ya bayar da wannan tabbacin ne a wata hira da ya yi da Dandalkura Radio International inda ya ce wannan gwamnati mai ci yanzu ta shirya tsaf domin gabatar da ayyukan da yawancin mutanen da suka zabe ta kan samar da kayayyakin more rayuwa a fadin jihar a karkashin aikin sabunta biranen.

Ya ce a matsayinsu na gwamnati ba ayyuka bane ba kawai da suka fara har ma da kammala duk wani aiki da magabata suka yi watsi da shi.

Ya bayyana cewa kyakkyawan tsarin mulkinsu yasa sun cimma nasarori da dama cikin shekaru biyu da aiwatar da ayyukansu.

Kwamishinan ya bayyana cewa lokacin da wannan gwamnatin ta hau mulki sai ta fahimci cewa cibiyoyin da dama a birane suna fuskantar abubuwan more rayuwa, inda suka ga lokaci yayi da mutane zasuci gajiyar shi.

Leave a Reply