Gwamnatin Jihar Adamawa Ya Karbi Al,luran Rigakafin Cutar Corona Dubu 59.

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

By Hassan Umar Shallpella, Adamawa
Gwamnatin jihar Adamawa ya samu rigakafin AstraZeneca na cutar corona dubu 59 daga gwamnatin tarayya ta hannun kwamitin fadar shugaban kasa kan cutar corona.

Mal. Bashir Ahmad sakataren gwamnatin jihar ya bayyanawa manema labarai cewa an ajiye rigakafin a cibiyar kiwon lafiya mataki na farko.

Jihar ta shirya kaddamar da rigakafin a ranar Litini 15 ga watan Maris, kuma za’a fara da ma’aikatan lafiya sai kuma gwamnan.

Ya kara dacewa gwamnatin jihar zata samar da wani hanya ga duk wanda yake da bukatar rigakafin zaiyi rajista kafin a masa rigakafin.

Daga karshe yace gwamnatin jihar zata tabbatar da an raba rigakafin yadda ya dace a fadin jihar.

Leave a Reply