Gwamnatin Jihar Adamawa Ranar Labara Ta Kaddamar Da Kudi Sama Da Biliyan 142 A Shekarar 2022.

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

majalissar zantarwa na gwamnatin jihar adamawa ranar labara ta kaddamar da kudi sama da biliyan 142 na shekarar 2022.

kwamishinan sadarwa, Dr Umar Garba Pella, ne ya bayyanawa manema labarai bayyan tattaunawar da gwamnan jihar Ahmadu Umaru Fintiri, ya jagoranta a gidan gwamnatin jihar dake yola.

tsarin aikin ya zama al’ada tun shigowar sabon gwamnatin jihar wajen tabbatar da cewa tsarin yadda ake gudanar da kudade sun tafi daidai da mafi yawan kasacen duniya.

ya kara dacewa, duk wani kashe kudi zai kasance cikin tsarin kudaden da gwamnatin ta kaddamar na 2022 wanda hakan zai duba tsarin yadda aka kashe su cikin shekarar.

kwamishinan ya kara dacewa, majalissar ta umarci kwamitin shirye-shirye, ma’aikatar kudi da sauran ma’aikatu dazasu bada gudunmawa domin aiki tare don gudanarwa da ayyukan.

ya kara dacewa majalissar ta kaddamar da naira biliyan 700 a kananan hukumomin Shelleng, Gombi, Lamurde, Girei, Numan, Mubi da Song don gyaran kayyakin aikin kiwon lafiya.

acewarsa, an samu Karin kudin, duba da yadda kudaden kayyayaki suka karu wanda da kudin naira biliyan 1.4 ne.

Leave a Reply