Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Gwamnan Jihar Rivers Nyesom Wike Ya Karyata Rushe Masallaci A Jihar

Rivers
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ya bayyana rahoton da ake yadawa cewa gwamnatinsa ta rushe masallaci a jihar inda yace kawai an shirya labarin ne dona bata masa suna.

Yayin da yake ganawa da manema labarai a gurin dake kan titin Biambo kusa da mahadar Mami Market Wike ya bayyana cewa babu wani masallaci a gurin kuma ba’a rusa komai ba.

Gwamnan ya kara da cewa ya samu wayoyi daga wasu muhimman yan Najeriya kan labarin mara tushe da ake yadawa a kafafen sadarwa.

Gwamnan ya kirayi musulman dake jihar Rivers dasu nuna masa inda aka rusa masallacin a jihar. San nan ya kiraye su da kar su bari yan siyasa suyi amfani dasu wajen batawa gwamnatin jihar Rivers suna.

Related stories

Leave a Reply