
By Ali Mohd Zanna
Gwamnan jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya farfesa Babagana Umara Zulum ya taya al’ummar jihar Borno murnar yin bikin sallah da azumi lafiya.
Ya bayyana cewa rahamar da aka samu a watan azumin insha Allah zata cigaba da kawowa jihar Borno da ma kasa baki daya zaman lafiya.
Zulum ya kara da cewa gwamnatinsa zata yi kokarin ganin ta kara kaimi kan kyakkyawan Mulki a jihar.
