Gwamnan Jihar Borno Ya Kafa Kwamiti Kan Gidajen Gwamnati Dake Birnin Maiduguri

Gwamnatin jihar Borno karkashin gwamna Babagana Umara Zulum ta kafa kwamiti na mutanen da zasu duba wadanda ke zaune a dukkanin gidajen gwamnati da gwamnatin jihar ta gina a birnin Maiduguri.

An kaddamar da kwamitin a gidan gwamnatin jihar inda aka nada Alh. Ibrahim Usman Ngulde a matsayin shugaban kwamitin sai Alh. Mustapha Ali Kori a matsayin sakatare inda aka basu sati biyu su kamala aikin nasu.

Yayin da yake gabatar da kwamitin farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana cewa dole gwamnati ta samarwa ma’aikatan ta gidajen zama inda koda sun bar aiki zasu zauna ba damuwa.

Haka nan ya kirayi yan kwamitin da suji tsoron Allah yayin gudanar da ayyukan su kuma su tabbatar da gidajen na ma’aikatan gwamnati ne ko ba nasu bane.

Gidajen sune rukunin 202,303,505,777 da 1000, inda yace gwamnati zata ci gaba da kula da kuma taimakawa ma’aikatar gidaje ta hanyar samar da hanyoyi da abubuwan more rayuwa.

Shugaban kwamitin ya godewa gwamnan da ya zakulo su don gudanar da wan nan aikin inda yace baza su bashi kunya ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *