Gwamnan Jihar Bauchi Yace Yankin Arewa Maso Gabas Ta Galabaita Da Rashin Tsaro.

Gwamna Bala Muhammad ya karbi bakwancin mambobin kwamitin majalisar dattawa kan gyaran kundin tsarin kasa na shekarar dubu 1 da dari 9 da 99 a gidan gwamnati dake Bauchi.

Gwmnan ya bukaci yan majalisar da su dukkan abin da ya dace domin magance matsalolin da ake fuskanta a kasra nan ta gyaran kundin tsain kasar.

Yace yankin arewa maso gabas ta canza ta bangaren rabon kasafin kudi, matsalar rashin tsaro, matsalar ayyukan agaji da sauran su, inda yace wannan matsala ne da majalisar ya kamata ta tattauna akai.

Yace yana kyautata zaton da irin kokarin sanatocin da suka fito daga yankin, aikin zai basu damar daidaita kalubalen da ake fuskanta a yankin.

Gwamnan yace Najeriya tana cikin wani yanayi na wuya musamman matasa, yayi kira ga majalisar da tayi kokari wajen aiwatar da kundin tsarin da gaskiya.

Tunda farko dai shugaban cibiyar kan gyaran kundin tsarin, sanata Abubakar Kyari ya bayyanawa gwamna Bala cewa ana sa ran wasu manya daga jihohin Bauchi, Borno da kuma Yobe zasu bayyana ra’ayoyin su game da lamarin domin cike ratar dake Tsakani.

Sanata Kyari wanda ke wakiltar Borno ta arewa yace bangarorin da za’a maida hankali akai sune tsaro, amfanin kasa, hadin kan yan Najeriya da rabewar iyakoki.

Sauran sun hada da samun yancin kai ga kananan hukumomi, hukumar zaben jiha, albashi mafi karanci, muhimmancin majalisar sarakunan gargajiya da sauran su.