Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Najeriya: Gwamnan Jihar Bauchi Ya Kaddamar Da Bikin Tara Kudi Don Taimakawa Tsofaffin Sojoji

bala
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan jihar Bauchi Bala Abdulkadir Mohammed ya kaddamar da bikin tara kudi don gudanar da bikin tunawa da ranar sojoji na shekarar 2020.

Yayin da yake jawabi a yayin bikin da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar ta Bauchi, gwamnan ya jaddada kokarin gwamnatinsa wajen habbaka rayuwar sojojin da iyalansu.

Haka nan ya tabbatar cewa gwamnatinsa zata cigaba da taimaka musu wajen inganta rayuwarsu kuma ya kirayi ma’aikatu da jama’a dasu yabawa gwamnati wajen kokarinta a wan nan bangaren don cigaban tsofaffin sojojin.

Gwamna Bala Mohammed ya bayyana cewa zai kafa wasu kwamishinonin a jihar kamar yadda aka bukata karkashin ma’aikatar tsaro.

A nashi jawabin shugaban taron Warrant Officer Idris Danjuma Ningi mai ritaya ya roki gwamnatin jihar data taimaka musu da abubuwan da suke bukata don su taimakawa hukumomin tsaro dake jihar wajen samun zaman lafiya.

Related stories

Leave a Reply