Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Gwamna Zulum Yaba Da Umarni Da A Gabatar Da Sunayan Dalibai Da Zasu Samu Gurbin Karato A Kasar Masar

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamna jihar Borno farfesa Babagana Umara Zulum ya umarci ma’aikatar manyan makarantu da kimiyya data gabatar da sunan daliban kimiyya domin sama musu gurbin karatu kyauta na karatun dagiri bangaren likitanci da sauran su a jami’ar Alkahira dake kasar Masar.

Zulum yaba da umarnin hakan bayan ya karbi rahoton kwamitin da aka nada a juli na 2020 wanda tsohon daraktan jami’ar farfesa Othman Kyari ke jagoran ta domin fiddo da tsare-tsaren a asibitin jami’ar Maiduguri da kolajin likitanci wanda dukka zasu bada damar karatun digiri na likitanci da sauran bangarorin ilimi.

Kyari yace kwamitin sun sha ziyartar jami’o’i da manyan makarantu domin gano yadda abubuwan suke kafin samar da mafita wanda tuni gwamna Zulum ya kaddamar da wasu.

Ya kuma ce kwamitin ta yi amfani da sunan Borno State College of Health Sciences wata kolajin kimiyyar lafiya, domin saukake wa jami’ar jiha wajen bada horaswa ga daliban kiwon lafiya dama likitoci.

Leave a Reply