Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Gwamna Zulum Ya Raba Naira Miliyan 325 Da Abinci Ga Magidanta 100,000 A Monguno

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya kai ziyara garin Monguno inda ya duba yadda ake rabon Naira miliyan 325 da abinci iri-iri ga magidanta sama da 100,000 da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu tare da hana su zuwa gonaki, kasuwanci da sauran hanyoyin rayuwa.

Monguno shine yanki mafi girma a arewacin Borno, a cikin yankin Najeriya na yankin tafkin Chadi, wanda ya fuskanci munanan hare-hare daga Boko Haram a cikin shekarun nan.

Magidantan da suka rasa muhallansu daga kananan hukumomin sun hada da Kukawa, Marte, Ngnazi da Guzamala a halin yanzu suna zaune a sansanonin da gwamnati ke iko da su a garin Monguno.

Zulum ya tashi daga Maiduguri zuwa Monguno a mota ranar Litinin, don kula da yadda za’ayi rabon kuɗade da kayayyakin abinci.

An rarraba buhunan hatsi, sukari ga magidanta dubu 65 da kuma 35,000 ga mata inda kowane magidanci ya karbi buhunan shinkafa uku, hatsin masara, da wake, yayin da kuma Naira N5,000.

Haka nan gwamna Zulum ya amince da wurin da za a gina Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya a Monguno, wanda Gwamnatin Tarayya ta amince da shi kwanan nan, sannan Gwamnan ya ziyarci Ministan Ilimi a watan Janairu, na wannan shekarar, tare alƙawarin samar da fili da duk wani tallafi da ake buƙata daga gwamnatin jihar Borno.

Leave a Reply