Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Gwamna Fintiri Ya Inganta Bangaren Ilimi A jihar,

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Hassan Umar Shallpella, Adamawa
Kwalejin noma dake Ganye na jihar Adamawa da aka samar da ita shekaru 28 da suka gabata har yanzu hukumar ilimi bata tabbatar da kwasa kwasan ta ba sakamakon rashin kayaki.

Mr. Aminu Kardu Tsigya mukaddashin shugaban kwalejin wanda ya bayyana haka ga manema labarai, ya nuna damuwar sa kan lamarin.

Yace kwalejin bazata iya kai ga matsayin tabbatar da kwasa kwasan ba sakamakon kalubalen da ta ke fuskanta.

Yayi kira ga gwamnatin jihar da ya taimakawa makarantar domin fuskantar kalubalen da ta addabi makarantar.

Yace duk da matsalolin da suke fuskanta, kwalejin ta yaye dalibai da dama wanda suke taimakawa cigaban jiha da kasa.

Yayi godiya ga gwamna Fintiri wajen inganta bangaren ilimi a jihar, yace yana da tabbacin gwamnan zai ceto kwalejin daga matsalar da take ciki.

Haka kuma yayi godiya ga Gangwari na Ganye Alh. Adamu Sanda na 2 da kuma al’ummar Ganye bisa taimako ga kwalejin.

Leave a Reply