Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Gwamna Buni Ya Bada Umarnin Bude Makarantu a Jihar Yobe

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya ba da umarnin sake bude makarantun kwana da aka rufe saboda sace daliban da aka yi kwanan nan.

An bayyana hakan ne a taron Majalisar Tsaro da aka gudanar a Damaturu, babban birnin jihar.

A cewarsa, sake budewar nada nasaba da a samu kammala karatun shekarar 2020/21 da ya wuce su.

Buni, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Idi Barde Gubana ya ce an rufe makarantun ne a ranar 28 ga Fabrairu, 2021 biyo bayan sace dalibai sama da 1,000 a jihohin Katsina, Zamfara, Kaduna da Neja.

Ya ce sake bude makarantun ya biyo bayan sake duba yanayin tsaro da hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki a jihar suka yi.

Ya kuma ce gwamnatin jihar ta dauki matakin da ya dace don kare rayuka da dukiyoyin mutane, gami da dukkan makarantun da ke fadin jihar.

A yayin da yake yi wa manema labarai bayani kan bude makarantun, Kwamishinan Ilimin Firamare da Sakandare, Dokta Mohammed Idriss ya bayyana cewa hukumomin tsaro za su kare makarantun tare da bada goyon baya da hadin gwiwar shugabannin makarantar, iyaye da masukula da yaran.

Leave a Reply