Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Gwamna Buni Ya Amince Da Nadin Mambobi 3 Na Hukumar Kula Da Shari’a Ta Jihar Yobe

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

From Hadiza Garba, Maiduguri

Mai Girma Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni ya amince da nadin mambobi 3 na Hukumar Kula da Shari’a ta Jihar Yobe a karo na biyu kuma na karshe a shekaru 5.

Sakataren yada labarai na Sakataren gwamnatin jihar Yobe Shuaibu Abdullahi ne ya bayyana haka, inda yace sabbin mambobin sun hada da Barista Yusuf Bala Haladu, Alhaji Ibrahim Gaji da Alhaji Baba Gishiwari.

Bugu da kari, gwamnan ya amince da nadin Barista Gambo Hussaini Jumbam don ya zama mukaddashin memba na Hukumar Kula da Shari’a don maye gurbin Barista Mohammed Gambo Gujba wanda wa’adinsa na 2 kuma na karshe zai zo karshe daga 16 ga Afrilu, 2021.

Sanarwar ta kuma kara da cewa dukkanin wadanda aka nada din zasu fara aiki ne nan take.

Leave a Reply