Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Fiye Da Mutane Biliyan Biyu Ne Ke Bukatar Tsaftataccen Ruwa Inji Majalisar Dinkin duniya

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Fiye da mutane biliyan 2 ke buƙatar ruwa mai tsafta kamar yadda Majalisar Dinkin Duniyata bayyana a ranar bikin Ranar Ruwa ta Duniya na 2021.

An fara gudanar da wan nan ranar ne daga Majalisar Dinkin Duniya don ƙudurin kiyaye ranar Ruwa ta Duniya a ranar 22 ga Disamba, 1992 inda daga baya aka maida ranar zuwa 22 ga Maris a matsayin Ranar Ruwa ta Duniya inda aka fara gudanar da bikin a duk duniya tun shekrar 1993.

Taken Ranar Ruwa ta Duniya na shekarar 2021 shine “Darajar Ruwa” kuma an zaɓi tane ne don nuna darajar ruwa a rayuwar mu ta yau da kullun.

Ana bikin ranar ruwa ta duniya kowace shekara a fadin duniya a ranar 22 ga watan Maris da nufin nuna mahimmancin ruwa da wayar da kan mutane game da matsalar ruwa da duniya ke fuskanta.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya, babban abin da ranar za ta fi mayar da hankali a kai shi ne a goyi bayan cimma burin ci gaba mai dorewa wanda shi ne na shida cikin kudirin majalisar na tsaftar muhalli ga kowa har zuwa shekarar 2030.

Leave a Reply