FARASHIN DANYEN MAI TATASHI A KASUWANNEN DUNIYA A SANADIYAR TAKUNKUMIN WASHINGTON KAN KASAR IRAN

A ranar litinin farashin kasuwar hada-hadar man fetur ta duniya ta tashi, saboda kasar Amurka ta fara harkar danyen man fetur tun bayan takunkumin da ta sanya wa kasar Iran a watan Nuwamba da ta gabata.
A zuwa yanzu farashin kamfanin ‘‘Texas Intermediate’’ na kasar Amurka ya kai dala saba’in da bakwai da digo talatin da uku kowace ganga guda sabanin dala 68.19 a baya.
Takunkumin da kasar Amurka ta sanya wa kasar Iran shi ne ya tada farashin man fetur a kasuwannin duniya.
Kamfanin ‘‘ENERGY CONSULTANCY’’ tace manyan masu cinikin kasashen Indiya, Japan, da kuma Korea ta Kudu sun fara janyewa daga alakar cinikaryar siyan danyen man fetur a kasar Iran.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *