EFCC Ta Kame Yan Najeriya 400 Da Laifin Zamba Ta Yanar Gizo A Cikin Watanni Uku Na Farkon Shekarar Nan.

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci Da Rashawa Abdulrasheed Bawa ya bayyana cewa Hukumar ta kame sama da matasa ‘yan Najeriya 400 da laifin zamba ta yanar gizo a cikin watanni uku na farkon shekarar nan.

Ya bayyana hakan ne a ofishinsa yayin karbar bakuncin wata tawaga daga jami’ar Abuja karkashin jagorancin mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Abdulrasheed Na Allah.

A cewar Shugaban Hukumar ta EFCC daga watan Janairun 2021 zuwa yau sun kame ‘yan Nijeriya sama da 400 da ake zargi da hannu a aikata laifuka daban-daban na yanar gizo ko kuma ci gaban laifuka masu alaka da damfara kuma hakan zai nuna muku yadda matsalar take.

Ya kuma ce kasa da awanni 48 da suka gabata sun kame mutane 18 a Abuja, wasu daga cikinsu daliban makarantun gaba da sakandare ne.

A yayin da yake nuna takaicinsa game da illar aikata laifuka ta yanar gizo yace hakan na taba mutuncin kasar.

Bawa ya ba da shawarar da a dinga horar da matasa, kuma jami’a na da muhimmiyar rawar da za ta taka wajen tabbatar da hakan.

Ya bayyana kwarin gwiwar cewa za a samu karin hadin kai tsakanin EFCC da Jami’ar Abuja a fannonin wayar da kai da dakile shigar matasa da aikata laifukan kudi.

shugaban na EFCC ya yaba da dadaddiyar alakar da ke tsakanin EFCC da Jami’ar ta Abuja, musamman kan kwasa kwasan karatun digiri na biyu a fannin binciken kwakwaf.

Leave a Reply